Connect with us

Labarai

Zargin Maita: Uwa da Ɗa sun rantse da Al’ƙur’ani

Published

on

Kotun shari’ar Musulinci mai lamba daya dake nan Kano ta rantsar da wata uwa da ɗan ta da Alkur’ani mai girma saboda zarginsu da laifin  ɓatawa wata wata mata da cewa ita Mayyace.

Tun da fari Rukayya Kabiru ita ce aka batawa suna kuma ita ce ta shigar da  makotan ta kara kan zargin maita da suke mata.

Rabi’atu Idris da Ɗanta Muhammad Idris ne wadanda ake kara har ma shi dan yayi ikirarin zai kashe Rukayya bayan kiranta da mayya da suke yi.

A zaman kotun na yau mai shari’a Munzali Tanko ya tambayi wadanda ake kara su biyu kan zargin da akeyi musu inda suka musanta dukka zargin da ake musu.

A nan ne mai shari’a ya nemi mai kara da ta kawo shaidun da za su tabbatar da cewa sun bata mata suna sai dai tace bata da shaidu, inda anan ne mai shari’a ya rantsar da su da Alkur’ani mai girma kamar haka.

mai shari’a Munzali Tanko Soron Dinki ya yi musu nasiha mai ratsa zuciya tare da gargadinsu cewa kada su bari wata fitina ta kara faruwa a tsakaninsu a matsayinsu na maƙota.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!