Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Zargin rashin ƙwarewa: An rufe asibitin Al-ziyadah clinic da ke Na’ibawa

Published

on

Hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar Kano PHIMA ta rufe wani asibiti mai zaman kansa mai suna Al-ziyadah clinic da ke unguwar Naibawa ƴan katako.

Rufe asibitin dai ya biyo bayan samun wani rahoto, na wasu dabi’u da ake yi a sibitin, da kuma rashin kula da marasa lafiya yadda ya kamata, baya ga shan miyagun kwayoyi.

Hakan na cikin wata Sanarwa da mai magana da yawon hukumar Abba Ɗalha ya raba wa manema labarai a yau.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an gano asibitin yana kula da majinyata masu tu’ammali da kayan maye, wanda kuma ya saɓa dokokin asibitin.

A cewar sanarwar, asibitin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala gudanar da bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!