Labarai
Zargin safarar ƙwaya: NDLEA na neman DCP Abba Kyari Ruwa a jallo
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, ta ce tana neman dakataccen kwamandan sashin yaƙi da miyagun ayyuka da ke aiki a ofishin babban sufeton ƴan sandan ƙasar nan DCP Abba Kyari ruwa a jallo.
Neman nasa dai ya biyo bayan zargin sa da hannu a cinikin hodar Iblis da nauyinta ya kai kilogiram 25.
Hukumar NDLEA ta bayyana Kyari a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a wani taron manema labarai da daraktan yaɗa labaranta Femi Babafemi ya gabatar a shelkwatarta da ke Abuja a ranar Litinin 14 ga Fabrairu, 2022.
Hukumar ta ce, ta ɗauki matakin ne bayan ƙoƙarin da ta yi na gayyatar sa domin amsa tambayoyi amma hakan ya ci tura.
NDLEA ta kuma tabbatar da cewa DCP Kyari na cikin mambobin ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya, a don haka yana buƙatar ya amsa tambayoyin daga hukumar.
You must be logged in to post a comment Login