Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin yawo: Wani uba ya kashe ɗan sa a Kano

Published

on

Ana zargin wani mutum ya kashe ɗan cikinsa ta hanyar yi masa dukan kawo wuka da tabarya a unguwar Rijiya biyu a ƙaramar hukumar Dala.

Da safiyar Litinin ɗin nan ne, mutumin mai suna Lawan ɗan asalin jihar Katsina ya kashe ɗan na sa bayan da ya kulle shi a ɗaki.

Wata maƙwabciyar mutumin ta shaida cewa “ Mun jiyo kururuwar Abba muna kwance lokacin da mahaifinsa yake dukansa, bayan mun zo kawo masa ɗauki sai muka tarar ya kulle dakin kuma yaki budewa”.

Haka kuma ta ce “Tun ba yanzu ba da ma mahaifin marigayi Abba ya jima yana yi masa irin wannan mugun dukan ta hanyar kulle shi a ɗaki saboda yana zarginsa da tafiya yawo wani sa’in ma yana kwana a waje”.

Alhaji Dan Iya Ahmad shi ne mai unguwar Rijiya biyu a Dala ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce “bayan an sanar da ni na isa gidan kuma na ganewa ido na yadda mahaifin ya kashe ɗan nasa ta hanyar dukansa da tabarya”.

Tuni dai rundunar ƴan sandan Kano ta bakin mai magana da yawun ta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce za su yi ƙarin bayani a nan gaba.

Yanzu haka dai an killace gawar marigayi Abba a Asibitin Murtala, kuma tuni jami’an tsaro suka cafke mahaifin marigayin bayan da ya yi ƙoƙarin guduwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!