Labarai
Zauren Hadin kan Malamai ya yi Allah-wadai da hukuncin Kotun ECOWAS

Zauren Hadin Kan Malamai da Kungiyoyin Musulmi na jihar Kano, ya yi Allah-wadai da hukuncin ganganci da Kotun Kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen Africa ta Yamma ECOWAS ta yi na sanar na neman Gwamnatin Nigeria kan ta soke dokar batanci ga Annabi SAW, da sunan wai sun ci karo da dabbaka hakkin Dan Adam na fadar albarkacin bakinsa.
Zauren, ya bayya hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun Sakatarensa Dakta Saidu Ahmad Dukawa
Sanarwar, ta ruwaito cewa, a wajen yanke wannan hukunci, Kotun ba ta yi la’akari da cewar kowace doka ta na da iyaka ba, musamman idan hakkin wani ya shiga hurumin wani daban.
ta kuma bayyana cewa, Kotun ba ta yi la’akari da manufar doka ta neman zaman lafiya da kaucewa daukar matakan ramuwar gayya ba.
” Kotun ba ta yi la’akari da tsarin mulkin kasashen da suke cikin hadakar kungiyar ba, wanda ya bai wa kowace kasa hurumin yin dokokin da suka dace da ita ba, sa’annan ya fifita Tsarin Mulkinta bisa sauran dokoki na ciki da wajen Kasar ba”.
” A dalilin haka Zaure ya na tir, da Allah-wadai, da wannan makahon hukunci,” a cewar sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, ” Zaure kuma ya na yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya yi azama wajen fitar da matsayar gwamnatinsa game da wancan hukunci inda ya ce, gwamnatin Jihar Kano ba za ta soke dokarta, ta hani ga batanci ga Annabi Muhammadu SAW, ba.”
” Matakin da gwamnan ya dauka ya yi kyau kuma ya cancanci yabo, kuma muna kira ga Limamai da Malamai da su yi amfani da mumbarinsu da majalisunsu wajen jan kunnen wannan Kotu ta ECOWAS, kan ta san matsayinta”, a cewar sanarwar.
You must be logged in to post a comment Login