Connect with us

Kiwon Lafiya

Zazzabin Lassa ya barke a jihar Kaduna

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da barkewar zazzabin da Beraye ke jawowa a yankin karamar hukumar Chikun.

Kwamishiniyar lafiya ta jihar Dr Amina Muhammad Baloni ce ta bayyana hakan inda tace wani dan shekara 36 da ya kamu da cutar an killace shi a a wata cibiyar kula da cututtuka masu illa a jihar.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai

Dr Amina ta tabbatarwa da al’ummar jihar ta Kaduna cewa an ware cibiyoyin kula da alumma domin jiran ko ta kwana.

Buhari Bai Damu Da Harkokin Lafiya Ba-Likitocin Yara

Gwamnatin Kano za ta fara karrama ma’aikatan lafiya

Tace sashin da Gwamnatin jihar Kaduna ta ware na musamman yana da ingantaccen kayan kulawa da marasa lafiya koda matsalar ta zazzabin beraye zai taso.

Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu

Kwamishinar lafiyar ta jihar ta Kaduna ta bukaci al’umma da su kiyaye tsafta da kuma rufe abinci yadda ya kamata da kuma kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa da gaggawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,655 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!