Connect with us

Labaran Kano

Kananan hukumomin jihar Kano za su ciyo bashin Naira Biliyan Goma Sha Biyar

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya aikawa majalisar dokokin jihar Kano da wata wasika da ke neman ciyo bashi ga kananan hukumomin jihar Kano arba’in da hudu.

Da ya ke karanta wasikar,   shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdul’aziz Garba Gafasa, ya ce, kananan hukumomin za su ciyo bashin ne don samar da kudade da za su yi amfani da su wajen shirin ba da ilimi kyauta da gwamnatin Kano ta kaddamar a shekarar da ta gabata.

“Kowace karamar hukuma za ta ciyo bashin naira biliyan dari uku da arba’in, a daya daga cikin bankunan kasuwanci na kasar nan.

Lauyoyi sun nemi majalisar Kano ta jingine batun dokar kafa masarautu 4

Majalisar Kano zata aiwatar da dokar cin zarafin bil adama

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga aiwatar da sabuwar majalisar sarakuna

Bayan karanta wasikar, shugaban majalisar Abdulaziz Garba Gafasa, ya tambayi mambobin majalisar, ko sun amince da a karbi wasikar da gwamna ya aiko da shi, wanda ba tare da bata lokaci ba, su ka amince da hakan.

Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano, Abdullahi Isah, ya ruwaito cewa, daga nan ne Kuma majalisar ta umarci kwamitin ta da ke kula da kananan hukumomi da ya je ya nazarci wasikar da ke kunshe da bayanan yadda za a ciyo bashin da  kudin ruwa da yadda za a rika biyan bashin.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,907 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!