Labarai
Zazzafar muhawara ta barke a zauren majalisar dattijai kan nada manyan hafsoshin tsaron Najeriya
Muhawarar ta barke ne a zaman majalisar na larabar nan 17 ga watan Maris.
Lokacin da Sanata Eyinnaya Abaribe ya gabatar da kudurin dokar kafa hukumar kula da sojoji ta kasa, da ke bukatar baiwa ko wane sashe na kasar nan wakilci a ciki.
“wannan bukata ta wa ta dace da sashe na 217 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999,” in ji Sanata Abaribe.
To sai dai ‘yan majalisar sun fafata muhawara tsakanin masu goyon baya da kuma wadanda ba sa goyon baya, inda shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya jefa tambaya ga mambobin majalisar don jin ra’ayoyinsu.
Daga bisani ne masu adawa da kudurin dokar suka yi rinjaye kuma Ahmad Lawan ya buga gudumar korar kudurin.
To sai dai daga baya Sanata Abaribe ya zargi shugaban majalisar da nuna son rai, inda ya buga misali da doka ta 73 da ta ba shi damar jayayya da wannan mataki na mafi rinjayen ‘yan majalisa.
You must be logged in to post a comment Login