Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya bai wa daliban CAS Tudunwada umarnin komawa CAS ta cikin birni don ci gaba da karatu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta umarci dalibai ‘yan kwalejin share fagen shiga jami’a da ke Tudunwada da su koma daukan darasi a kwalejin share fagen shiga jami’a ta CAS da ke nan cikin birnin Kano.

Shugaban kwalejin share fagen shiga jami’ar ta Tudunwada, Dr. Yusuf Musa Kibiya ne ya bayyana haka yayin zantawa da tashar freedom radio.

A cewar sa, daukar wannan mataki ya zama wajibi don bai wa daliban damar ci gaba da karatunsu, maimakon zama a gida.

A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Kano ta dauki matakin rufe wasu makarantun gaba da sakandire ciki har da kwalejin share fagen shiga jami’ar ta Tudunwada sakamakon ci gaba sace dalibai da ke wakana a wasu jihohi da ke yankin arewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!