Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan Adaidaita sahu za su gane shayi ruwa ne – Baffa Babba

Published

on

Shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Ɗanagundi ya ce matuƙa baburan adaidaita sahu a Kano za su gane shayi ruwa ne.

Baffan ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ta shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio, kan yajin aikin da Ƴan Adaidaitar suka tsunduma.

Ya ci gaba da cewa, wannan yajin aiki ƙilu ce za ta jawo bau ga masu adaidaitar.

Baffan ya kuma ce, rashin fitowar su a yau, ya sanya ana bin dokokin titi a Kano.

A Litinin ɗin nan ne aka wayi gari da yajin aikin Ƴan Adaidaitar bayan da suka zargi KAROTA da cusguna musu, kan batun sabinta rajista.

Sai dai dama tun a baya KAROTA ta sha musanta hakan tana mai cewa, abin da take yi gyara kayanka ne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!