Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun hallaka wani malamin Izala ta hanyar rataya

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun hallaka wani limamin ƙungiyar Izala ta hanyar rataya a jihar Kebbi.

Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne a daren Jumu’a inda wasu da ba a san ko su wanene ba suka rataye malamin a ɗakin da yake ganawa da baƙi a unguwar Bayan Kara da ke Birnin Kebbi.

Mataimakin shugaban kwamitin yaɗa labaran ƙungiyar Izala ta Intanet na ƙasa Engr. Adamu Attahiru ya yiwa da wakilin mu Bashir Sharfaɗi ƙarin bayani kan lamarin.

Engr. Attahiru ya ce, Marigayin sunan sa Malam Abubakar Zaki Tari, kuma shi ne limamin unguwar Bayan Kara, sannan mataimakin sakataren majalisar ƴan agajin Izala na jihar Kebbi, baya ga haka marigayin ma’aikacin lafiya ne a Asibitin tarayya da ke Birnin Kebbi.

Marigayin ya rasu ya bar mahaifiyar sa da mata biyu da ƴaƴa da dama.

Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bakin mai magana da yawunta DSP. Nafi’u Abubakar sai dai bai yi ƙarin bayani ba, inda ya ce suna ci gaba da bincike a kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!