Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun kashe mutane 7 tare da sace Dagaci a Kano

Published

on

Ƴan bindiga sun hallaka mutane Bakwai a garin Ƙarfi na ƙaramar hukumar Takai da ke Kano, tare da sace Dagacin garin.

Wani ɗan uwan Dagacin da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatarwa da Freedom Radio wannan al’amari.

Ya ce, “Ƴan bindigar sun kutsa kai garin a kan Babura cikin daren Asabar, inda suka yi awon gaba da Dagacin”.

Sai dai sun samu tirjiya daga mutanen garin waɗanda suka yi ƙoƙarin kuɓutar da Dagacin, abin da ya sa ƴan bindigar buɗe wuta kan mai uwa da wabi inda suka harbe mutane Bakwai.

Daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su sun haɗa da Tasi’u Birniyo da Ali Yahaya da Hashimu Amo da kuma Sadiƙu Hussaini.

Sai Amadu Bakin Ɗanlanbu da Bala Audu sai Shu’aibu Agwarmaji.

Freedom Radio ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ƴan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto haƙanmu bai cimma ruwa ba, kasancewar bai ɗauki kiran wayar da muka masa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!