Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Ƴan bindiga sun sake kai hari a Kaduna

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane takwas tare da jikkata hudu a wani hari da suka kai a kananan hukumomin Kajuru da Kachia na jihar Kaduna a jiya Talata.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Arwan ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sa, ‘yan bindigar sun tare kan hanyar Kaduna zuwa Kachia daidai kauyen Kadanye na karamar hukumar Kajuru sannan suka bude wuta kan wasu matafiya da ke cikin mota kirar Bas.
Lamarin da yayi sanadiyyar rasa ran mutane biyar tare da jikkata mutane uku nan take.
Haka zalika, wasu ‘yan bindigar sun sake tare hanyar daidai garin Doka inda suka harbe direban wani mota, tare da jikkata wasu.
Arwan ya ce, a kauyen Inlowo na karamar hukumar Kachia ‘yan bindigar sun afkawa makiyaya inda suka hallaka wani mai suna Alhaji Haruna Ibrahim tare da yin awon gaba da shanu 180.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!