Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ƴan bindiga sun saki fursunonin da ke tsare a gidan gyaran hali na Oyo

Published

on

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari gidan gyaran hali na Abolongo da ke garin Oyo.

Ƴan bindigar sun kai harin a daren ranar Juma’a tare da sakin fursunonin da ba a san adadin yawansu ba a gidan yari.

Olarewaju Anjorin shi ne jami’in hulɗar da Jama’a na hukumar kula da gidajen yari reshen Jihar Oyo, ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Asabar a zantawar sa da manema labarai a Ibadan.

Anjorin ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 9.50 na daren Juma’a.

Rahotonni sun tabbatar da cewa maharan na dauke da muggan makamai tare da razana masu gadin gidan sannan suka kutsa kai ciki tare da sakin fursunonin.

“Ina nan a yanzu tare da Kwanturola da wasu manyan jami’an kula da gidan yarin don tantance ɓarnar da aka yi wa gidan”.

“Yanzu, ba za mu iya tantance adadin fursunonin da aka saki da waɗanda suka jikkata ba, amma tabbas nan gaba zan yi muku karin bayani” a cewar Anjorin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!