Connect with us

Labarai

Ƴan bindigar da suka sace ɗalibar BUK sun buƙaci miliyan 100 kuɗin fansa

Published

on

Ƴan bindigar da suka sace ɗalibar jami’ar Bayero mai suna Sakina Bello sun nemi kuɗin fansa na naira Miliyan ɗari kafin sakin ta, kamar yadda jaridar daily trust ta rawaito.

Tun a ranar Talata ne ƴan bibdigar suka sace ɗalibar da misalin ƙarfe uku na yamma a cikin baburin adaidaita sahu, tsakanin unguwar Janbulo da Rijiyar Zaki jim kaɗan bayan fitowarta daga gida.

Sakina ɗaliba ce mai shekaru 23 a tsangayar nazarin harkokin lafiya { Botany} kuma tana shekara ta uku a karatun ta.

Ƴan bindigar dai sun kira ɗan uwan Sakina da misalin ƙarfe 9 na dare ranar tare da tabbatar da cewa sune suka ɗauke ta, a don haka za su kira ranar laraba.

Sai dai rundunar  ƴan sandan jihar kano ta tabbatar da sace ɗalibai ta bakin mai magana da yawunta DSP Abdulahi Haruna Kiyawa.

Kiyawa ya ce, su na ƙoƙarin ganin an kuɓutar da Sakina Bello nan ba da jimawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!