Connect with us

Addini

Zauren malamai ya bukaci majalisar Kano ta karbe gini ko fili da wasu suka mallaka na masallacin waje dake fagge

Published

on

Zaurin hadinkan Malamai da kungiyoyin musulinci na Kano ya yabawa majalisar dokokin jihar Kano dangane da dakatar da ci gaba da gine harabar masallacin waje dake Fagge.

Babban sakataren zauren Dakta sa’idu Ahmad Dukawa ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radiyo a ranar Laraba 06 ga watan Oktobar 2021.

Zauren ta cikin sanarwar ya kuma bukaci majalisar dokokin, data karfe duk wani gini ko fili da wasu mutane suka mallaka na masallacin.

Sa’idu Ahmad Dukawa ya ce masallacin na daya daga cikin wuraren da al’ummar musulmi sukafi bukatar sa.

Zauren ya kuma bukaci al’umma da su yi hakuri su bibiyi yadda zata kasance da masallacin a yanayi na bin doka da oda.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!