Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan kasuwar sabon Gari sun bukaci Gwamnati ta samar musu da motar kashe Gobara

Published

on

Kungiyar Kwankwasiyya Electronics Abubakar Rimi Market sun buƙaci Gwamnatin jihar Kano da ta samar musu da motocin kashe gobara domin gujewa matsala musamman ta tashin gobara a cikin kasuwa.

Shugaban ƙungiyar Magaji Umar Alkantara ne ya bayyana hakan yayin taron addu’a da ƙungiyar ta gabatar domin taya murnar samin nasara da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu a kotun ƙoli.

Ka zalika shugaban ya kuma nuna goyon bayan su bisa ga jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da bayar da haɗin kai domin samar musu da ci gaban kasuwar ta Sabon Gari.

Da yake jawabi ɗaya daga cikin dattawan kasuwar, Alhaji Sani Dankaka Mai Fanta ya bayyana kira yayi ga gwamnati wajen ƙara ingata harkar kasuwanci a kano da samarwa da matasa hanyoyin dogaro da kai.

  1. Da yake Jawabi ɗaya daga cikin Jagororin kungiyar, Muhammad Rabilu Ahmad wanda aka fi sani da Ustazun Kwankwasiyya ya bayyana cewar sun shirya wannan addu’a ne domin taya gwamna Abba Kabir Yusif murnar samin nasara da kuma tunatar da shi wajen samarwa da Al’ummar kano ci gaba a ɓangarori daban-daban na rayuwa.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!