Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan majalisar wakilai na PDP guda 4 sun koma APC.

Published

on

Wasu ƴan majalisar wakilai guda huɗu ƴan asali jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Mambobin na PDP sun sanar da sauyin sheƙa daga PDP zuwa APC ne yayin zaman majalisar a yau talata.

Waɗanda suka sauya sheƙar sune: Bello Hassan Shinkafi, Ahmed Bakura, Ahmed Shehu da kuma Suleiman Gumi

Ta cikin wata wasika mai ɗauke da sa hannun ɗan majlaisa Suleiman Gumi wanda aka karanta yayin zaman majalisar a yau talata, ƴan majalisar sun ce sun yanke shawarar barin jam’iyyar PDP ce sakamakon irin rikicin cikin gida da ya dabaibayeta, wanha ya kai ga uwar jam’iyyar ta ƙasa ta rushe shugabancin jam’iyyar a jihar.

Rahotanni sun ce tun farko dama mambobi shida na jam’iyyar  PDP a majalisar ta wakilai sun amince su sauya sheƙa tare da gwamna Bello Matawalle.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!