Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun bankaɗo gidan da ake ajiyar makamai a Kano

Published

on

Ƴan sanda sun bankaɗo gidan da ake ajiyar makamai a Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun bankaɗo wani gidan a garin Wangara na ƙaramar hukumar Rimin Gado.

An samu bindigogi ƙirar AK47 da kuma harsasai a gidan.

Tuni ƴan sanda suka cafke mai gidan Abubakar Isma’il ɗan shekara 30, inda suka shiga faɗaɗa bincike.

Kiyawa ya ƙara da cewa, binciken da suka gudanar zuwa yanzu ya nuna cewa Abubakar ɗin na aikata ayyukan ta’addanci tare da haɗin gwiwa da wasu ƴan ta’adda na maƙotan jihohi.

“Yana basu bindigogi su je wasu yankunan Katsina da Kaduna su kai harin ta’addanci, mun same su da hannu cikin aikata laifuka da dama” a cewarsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!