Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan Sanda sun far wa wakilan Daily Trust da BBC a kotun sauraren zaɓen gwamnan Kano

Published

on

Jami’an ƴan sanda sun far wa ’yan jaridar kafofin yada labaran Daily Trust da takwaransa na BBC a yayin da suka ke daukar rahoto a kotun sauraron kararrkin zaben gwamnan Kano, wadda a yau Laraba za ta yanke hukunci.

Zahraddeen Lawan na BBC da Salim Umar Ibrahim na Daily Trust, sun fuskanci hakan ne daga ’yan sandan da aka girke a wurin da kotun za ta yi zaman.

Da farko ’yan sandan sun umarci ’yan jaridar su yi nesa da baya da kimanin mita 10.

Ana cikin haka ne wasu daga cikin jamia’n tsaro suka fara cin mutuncin ’yan jaridar, wai suna daukar hoto.

’Yan sandan sun yi cakumi wakilin BBC suna kokarin kwace wayarsa daga aljihunsa,a yayin da wasu suka nemi kwace wayar takwaransa na Daily Trust, inda a garin haka suka fasa fuskar wayar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!