Labarai
Ƴar Kunar baƙin Waketa hallaka mutane 24 a Borno

Kimanin mutane 24 ne rahotanni suka ce sun mutu bayan wata ƴar ƙunar baƙin Wake ta kai hari a wani wurin cin abinci da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.
Zagazola Makama, wani manazarci kuma mai bibiyar ayyukan yaƙi da ƴan tada ƙayar baya da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a, inda wasu da dama suka samu munanan raunika.
Shafin jaridar ta Zagazola Makaman, ta ruwaito cewa ƴar ƙunar baƙin waken ta tayar da Bam ɗin ne l a wurin dafa abinci.
Haka kuma ta ce, gawar ƴar ƙunar baƙin Waken ta tarwatse ne sakamakon fashewar Bam ɗin, inda aka tsinci kanta kawai.
Ya ce, an ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiyar gawarwaki, yayin da waɗanda suka jikkata aka kai su wani asibiti da ke kusa, inda suke karbar magani.
Tawagar tsaro ta hadin gwiwa wadda ta hada da sojoji da ‘yan sanda da rundunar hadin gwiwa ta farar hula ta CJTF, da mafarauta sun ziyarci wurin da tashin Bam din ya faru.
Sanarwar ta ce, tun daga lokacin an killace yankin yayin da aka tsaurara matakan tsaro a fadin Konduga domin hana kai hare-hare.
Har yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar Borno ba ta ce uffan ba kan faruwar lamarin.
You must be logged in to post a comment Login