Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 Ɓacin rana: Ɗan sanda ya harbe abokin aikinsa a Kano

Published

on

Wani ɗan sanda ya harbe abokin aikinsa a caji ofis na garin Warawa da ke Kano.

Al’amarin ya faru ne a ranar Talata da dare, inda Insfekta Ya’u Yakubu ya harbe Sajan Basharu Alhassan sakamakon saɓani da suka samu.

Ƴan sanda sun garzaya da shi asibitin garin Wudil inda a nan rai yayi halinsa.

Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Ya ce, tuni Kwamishinan ƴan sanda ya bada umarnin a dawo da Insfekta Ya’u Yakubu Shalkwatar ƴan sanda domin ci gaba da bincike.

Rahotanni sun nuna cewa a baya an yita jita-jita kan saɓani tsakanin ƴan sandan biyu na zargin ɗaya na neman matar ɗaya.

Sai dai DSP. Kiyawa ya musanta hakan yana mai cewa, ɗan sanda ya harzuƙa ne kan dariyar da marigayin yayi masa dangane da maganar sauyin wajen aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!