Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Abin tausayi: Halin da masu larurar laka ke ciki a Kano

Published

on

Ƙungiyar masu lalurar Laka a Kano ta koka kan yadda jama’a ke mayar da su saniyar ware ko kuma suke kallonsu a matsayin mabarata.

Shugaban kungiyar Injiniya Danladi Haruna ne ya bayyana hakan, ta cikin shirin “Duniyar mu a yau” na Freedom Radio.

Injiniya Danladi wanda shi ma ɗaya daga cikin masu fama da lalurar ya ce “Masu lalaurar laka na fuskantar barazana a wurin Al’umma, ta hanyar ƙyamatar su, abinda ke sanya tsoro ga masu lalurar suke gudun fita cikin jama’a saboda da zarar sun shiga za’ayi tunanin neman taimako ne ya kawo su”.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana damuwar sa kan ƙaruwar masu fama da lalurar ciki har da ƙananan yara, har ma ya ce, “A baya za a iya ƙirga waɗanda ke ɗauke da lalurar saboda rashin yawan su, amma a yanzu abin ya wuce lissafi, inda a yanzu haka a asibiti ɗaya a Kano a na samun masu cutar sama da dubu hudu, ga kuma rashin kudin magani”.

Dalilan da suke haifar da lalurar Laka:

Injiniya Danladi ya ce kashi 70 na dalilan da ke jawo lalurar shi ne hadarin mota, sai kuma wadanda ake Haifa da shi.

“Mun lura cewa ɗaukar abu mai nauyi, da faɗowa daga kan bishiya da yin hatsarin mota da kuma rashin ɗaukar wanda yayi hatsari cikin ƙwarewa da kuma naushin mutum a wuya ko dukan sa a gadon baya duk suna janyo taɓuwar Laka” in ji Injiya Danladi.

Injiya Abdullahi Danladi ya koka kan rashin samun tallafi yadda ya kamata ga masu lalurar kasancewar ta tana da wuyar magani da kuma tsada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!