Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

RAHOTO: NAPTIP ta ceto mutane ɗari 3 a cikin mako 4

Published

on

Hukumar yaƙi da safarar bil-adama ta ƙasa reshen jihar Kano ta ceto mutane 300 da aka yi safarar su zuwa ƙetare.

NAPTIP ta ce, an ceto adadin mutanen ne cikin makwanni hudu da suka gabata.

Mai magana da yawun hukumar Malam aliyu Abba kalli ne ya tabbatar da hakan ga Freefom Radio.

“Mun samu nasarar ceto su ne, lokacin da aka yi yunkurin ficewa da su zuwa kasashen ketare, kuma mafi yawa daga cikinsu ƴan mata ne da samari” in ji Kalli.

Sai dai ya alaƙanta talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa ne ya ke haifar da matsalar yawaitar safarar mutane, wanda da hakan ake yaudarar su.

Kalli ya kuma ce, “Mutanen da suka yi yunkurin fataucin mutanen sun so yin amfani da barayin hanyoyi ne a jihohin Jigawa da Katsina, sai dai 80 daga cikin su anyi nasarar kubutar da su ne bisa tallafin jami’an ‘yan sandan Jamhuriyar Nijar, inda tuni mutum 5 cikin masu safarar suka shiga hannun mu”.

NAPTIP ta ce, wananna ne ya kawo adadin waɗanda aka kubutar daga hannun masu safarar bil’adam ya kai ɗari 6 daga farkon 2021 zuwa yanzu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!