Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ɗan zago ne halastaccen shugaban APC – Ɗan Sarauniya

Published

on

Tsohon Kwamishinan ma’aikatar ayyuka Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan sarauniya ya ce har yanzu Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne halastaccen shugaban jam’iyyar APC a Kano.

Ɗan sarauniya ya bayyana hakan a wani sauƙin murya da ya aikewa Freedom Radio.

Ɗan sarauniya ya ce “Zaɓe an yi an gama kuma tuni muka samu nasara ta hanyar lashe zaɓen da Ɗan zago yayi”.

“Kamar yadda ake jin raɗe-raɗe akwai inda aka yi zaɓe, amma fa gurguntacce dan takara ne, domin bai bi tsarin shiga takara ba da kuma tsarin dimukuraɗiyya”.

Ya ci gaba da cewa “Mu dama akwai ƴan takara 2 kuma sun janye wa Ɗan zago wanda hakan ya bashi damar zama zaɓaɓɓen shugaban jam’iyyar APC”.

Ɗan sarauniya ya kuma ce a yanzu za su tattara hankali wajen dawo da martabar jam’iyyar APC da kuma samun ƙaruwar magoya baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!