Labarai
Ƙananan hukumomi sun cinye sama da naira biliyan 40 na ƴan fansho – Ƙungiyar ƴan fansho
Ƙungiyar ‘yan fansho ta jihar kano ta zargi ƙananan hukumomi da hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar SUBEB da cinye kuɗaɗen fansho.
A cewar kungiyar sama da naira biliyan arba’in da huɗu na kuɗaɗen tsoffin ma’aikata suka cinye tsawon lokaci.
Shugaban kungiyar Kwamared Salisu Ahmad Gwale ne ya bayyana bayan kammala shirin “Barka Hantsi” na tashar Freedom radio.
Kwamared Salisu Ahmad ya ce, ƙungiyar su ba ta hana bayar da kuɗaɗen yan Fansho ba, sai dai hana ruwa gudu da ƙananan hukumomin ke yi da kuma SUBEB.
Shugaban kungiyar ƴan fansho na jihar Kano, ya ce mutanen da ya kamata su rika zuwa karbo kuɗaɗen basa yin aikin su yadda ya kamata, wanda ya bayyana hakan a matsayin wata babbar matsalar da ake samu a bangaren wawure kuɗaɗen
Kwamared Salisu ya kuma ce, tun ɗaga shekarar 2007 kananan hukumomin basa biyan kuɗaɗen ƴan fansho yadda ya kamata, wanda kuma a lokacin shugabancin ƙungiyar ba shi da yunƙurin magance matsalar.
You must be logged in to post a comment Login