Ƙetare
Ƙasashen ƙungiyar AES sun buɗe bankin zuba jari

Ƙasashen ƙungiyar Alliance of Sahel States AES, wato Burkina Faso, Nijar da Mali sun buɗe bankin zuba jari da ci-gaba domin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da ci-gaban tattalin arzikin yankin.
Ministan Tattalin Arziki da Tsare-Tsare na Burkina Faso Aboubakar Nacanabo ya sanar da cewa sun saka Dala Miliyan 895 a cikin bankin a matakin farko, bayan ganawar da ya yi da takwarorinsa na ƙasashen Mali da Jamhuriyar Nijar.
A watan Mayun da ya gaba ne, ƙasashen uku suka sanar da wani gagarumin shiri na kafa bankin zuba jari da zai riƙa daukar nauyin gudanar da manyan ayyukan more rayuwa da ci-gaba na ƙasashen uku.
You must be logged in to post a comment Login