Labarai
Ƙasashen Afirka da Ƙungiyar Tarayyar Afrika sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a Qatar

Ƙasashen Afirka da Ƙungiyar Tarayyar Afrika sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai ranar Talata kan shugabannin Hamas a Qatar, suna masu gargaɗin cewa ta keta ‘yancin kan ƙasar.
Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUC) ya yi gargaɗin cewa harin zai iya barazana ga yanayi mai rauni da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya.
Mahmoud Ali Youssouf ya yi nuni da rawar da Qatar ke takawa a wajen shiga tsakani na diflomasiyya yana mai kira da “a sabunta tattaunawa domin samun zaman lafiya na adalci mai ɗorewa a Gabas Ta Tsakiya”.
Ministan Harkokin Wajen Masar ma ya bayyana harin na Isra’ila a matsayin “tsabar keta dokar ƙasa da ƙasa da kuma ‘yancin kan ƙasa
You must be logged in to post a comment Login