Labarai
Ƙundin tsarin mulkin Najeriya da Abacha ya tsara ya fi na yanzu dacewa da ƙasar nan– Ngige
Ministan ƙwadago da samar da aikin yi, Dr Chris Ngige, ya ce, da Najeriya ta rungumi ƙundin tsarin mulkin da gwamnatin mulkin soji ta janar Sani Abacha ta tsara a 1995, da ba a shiga matsalolin ƙundin tsarin mulki da ƙasar nan ke fuskanta a wannan lokaci ba.
Mista Ngige ya bayyana hakan ne yayin zantawa da gidan talabijin na Channels.
Ya ce, ƙundin tsarin mulkin da gwamnatin Abacha ta tsara ya amince da wa’adin shekaru biyar-biyar ne kacal ga duk shugaban ƙasa kuma mulki zai rika juyawa tsakanin shiyyoyin ƙasar nan guda shida.
Ministan ya kuma ce, har gobe shi yana da ra’ayin cewa, ƙundin tsarin mulki da gwamnatin Abacha ta tsara, ya fi dacewa da Najeriya fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu.
You must be logged in to post a comment Login