Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙungiyar ƴan Jarida ta yiwa Doguwa martani kan zargin cin zarafin mambanta

Published

on

Ƙungiyar Ƴan Jarida ta ƙasa reshen jihar Kano ta nuna damuwarta kan zargin Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa da cin zarafin wani ɗan jarida a Kano.

Hakan na cikin sanarwar da Sakataren ƙungiyar Comrade Abba Murtala ya fitar.

Sanarwar ta ce, bata ji daɗin yadda Alhassan Ado Doguwa ya muzanta da cin zarafin mambanta Abdullahi Yakubu, wakilin jaridar Leadership lokacin da Doguwan ya kira taron manema labarai a gidansa.

NUJ ta ce, tana fatan tunda lamarin ya je gaban kotu za a yi kyakkyawan bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Ta kuma ja hankalin ƴan siyasa kan sun sani ƴan jarida abokan tafiya ne wajen cimma nasarar dimokraɗiyya.

Sanarwar ta kuma ce, mambobinta ba zasu ja da baya ba, za su ci gaba da aikinsu cikin ƙwarewa tare da bin doka da oda.

Labarai masu alaka:

Shugabannin ƙananan hukumomin Kano 44 sun yi Tir da Doguwa

Tasirin Kwankwaso a Kano kaɗai ya ishe mu – Saƙon Doguwa ga Ganduje

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!