Labarai
Ƙungiyar Arewacin Najeriya CNG ta buƙaci gwamnati da ta kuɓutar da Daliban Jami’ar Gusau da aka sace
Gamayyar Kungiyoyin Ɗalibai na Arewacin Najeriya “CNG” Ta ɓuƙaci gwamnatin Jihar Zamfara da gwamnatin tarayya da tayi ƙoƙarin kuɓutar da Daliban Jami’ar Tarayya Gusau da aka Kwashe
Gamayyar kungiyoyin Arewa CNG ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da gwamnatin jihar Zamfara da su yi hakuri, su fuskanci kalubalen tsaro da kuma tabbatar da ganin an dawo da daliban jami’ar da aka sace.
Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin da suke ganawa da ƙaramin Ministan Tsaro Alhaji Bello Matawalle da Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello sai shugaban Jami’ar tarayya ta Gusau Farfesa Mu’azu Abubakar kan yadda za’a kuɓuto da ɗaliban
Har ila yau, gamayyar ta lura da cewa aiyukan ta’addancin sun ƙara ƙamari a sassan jihar ko a gaban jami’an tsaro, wanda hakan ke nuni da cewa cin hanci da rashawa yana kara tasiri a cikin jami’an tsaron.
Gamayyar kungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin da ta kai ziyara garin Gusau da nufin samar da hadin kai da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Zamfara da hukumomin tarayya domin gudanar da ayyukan kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar da ma Arewa baki daya.
Da yake jawabi ga jami’an gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar, kakakin gamayyar CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce al’amura a jihar Zamfara sun kara ta’azzara saboda rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara, wanda hakan ke haifar da zargi tsakanin bangarorin biyu.
A cewarsa, lamarin ya kara jefa jama’a cikin rudani da ƙara ta’azzara kalubalen tsaro a jihar.
Kungiyar ta ce abin takaici ne maimakon a hada kai wajen magance matsalar tsaro, amma bangarorin biyu sun koma nuna yatsa ga juna.
You must be logged in to post a comment Login