Labarai
Ƴan bindiga sun ƙone gidan shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara
Wasu ƴan bindiga sun ƙone gidan shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya a ƙaramar hukumar Zurmi.
Shugaban kwamitin harkokin tsaro na majalisar Alhaji Abdullahi Shinkafi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar sa, ƴan bindigar sun shiga yankin ne tare da cinnawa gidaje wuta ciki har da gidan shugaban majalisar.
A cewar sa, harin nasu ya zo ne sakamakon yadda sojoji suka buɗe musu wuta a ƴan kwanakin nan musamman ma a yankin na Zurmi.
Shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Shinkafi bai yi ƙarin haske kan ko an rasa rayuka sanadiyyar wutar ba, amma ya ce tuni gwamnatin jihar ta bada umarnin akai ɗaukin gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login