Labarai
Ƴan bindiga sun afka wa tawagar gwamnatin Zamfara
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewar ƴan bindiga sun buɗe wuta ga tawagar da gwamnatin jihar ta aika zuwa Katsina.
Farmakin yayi sanadiyyar rasa ran mutum guda.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya fitar a daren Litinin.
Tawagar ta je Katsina ne domin miƙa ƴan mata 26 da aka kuɓutar daga ƴan bindiga ga gwamnati.
Labarai masu alaƙa:
Da ɗumi-ɗumi: An ceto ƴan mata dagahannun ƴan bindiga a Zamfara
Gwamnatin Katsina ta karɓi ƴan matan da aka kuɓutar a Zamfara
Sanarwar ta ce, yanzu haka ƴan sanda sun shiga bincike kan lamarin.
You must be logged in to post a comment Login