Labarai
Ƴan bindiga sun hallaka Hakimin garin Dogon Daji

Wasu ƴan bindga ɗauke da makamai sun afka wa garin Dogon Daji da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, tare da hallaka hakimin garin.
Shugaban ƙaramar hukumar Tsafe Garba Shehu Tsafe ya tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Litinin.
Ya ƙara da cewa a wunin ranar ƴanbindigar sun tare wasu hanyoyi a yankin da ke kai wa zuwa Gusau.
Shugaban ƙaramar hukumar ya alaƙanta ƙaruwar hare-haren yankin da sluhun da ake yi a jihar Katsina mai makwabtaka.
Ko da a baya bayan nan dai Rahotanni daga karamar hukumar Kanam da ke Jihar Filato na nuna cewa an samu gawar Sarkin Ƙauyen Shuwaka, Mallam Hudu Hassan Barau, wanda ’yan bindiga suka sace kusan mako guda da ya wuce.
Malam Hudu, wanda shi ne Dagacin Shuwaka a gundumar Kyaram, cikin al’ummar Garga, an gano gawarsa ne bayan kwanaki shida da ’yan bindiga suka yi awon gaba da shi.
You must be logged in to post a comment Login