Labarai
‘Ƴan bindiga sun hallaka mutane biyu a Kano
Ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane biyu a ƙaramar hukumar Rano.
Ƴan bindigar sun afkawa wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Rano da Garin Malam a daren Alhamis.
Garuruwan da suka afka wa sun haɗa da garin Dumawa da Garin Babba da kuma ƙauyen Gadar Jakai da ke ƙaramar hukumar Garin Malam.
Babban Kwamandan jami’an sintirin Bijilante na jihar Kano Muhammad Kabiru Alhaji ne ya bayyana hakan da yammacin ranar Juma’a.
Mutane biyun da suka rasa ransu sun haɗa da wani da ake kira da Ɗan Bunkure da kuma wani mai gadi da ake kira Ɗan Kadawa.
Kwamandan ya ƙara da cewa, ƴan bindigar da ke addabar wasu ƙauyuka a Kano sun shigo ne daga jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna, inda suka yadda zango a ƙaramar hukumar Rano.
Ya ci gaba da cewa, sun bi sahun ƴan bindigar ne bayan rahoton da suka samu na harin da suka kai garin Rurum a ƙaramar hukumar Rano.
Sai dai a daren ranar Alhamis ƴan bindigar sun sake ɓulla a garin Mudawa da ke ƙaramar hukumar Garin Malam, inda jami’an Bijilante suka koresu.
Daga nan kuma sai suka sake ɓulla a ƙauyen garin Babba, inda a nan ma suka yi ba-ta-kashi da ƴan bindigar wanda daga bisani suka arce.
You must be logged in to post a comment Login