Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun hallaka wani magidanci da ƴaƴansa a Zamfara

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun hallaka wani magidanci da ƴaƴansa biyu a garin Tsafe da ke jihar Zamfara.

Wani makusancin marigayin ya shaida wa Freedom Radio cewa, ƴan bindigar sun shiga gidan marigayin mai suna Alhaji Sani Kwama inda suka shiga saransa da ƴaƴansa biyu da makamai.

Yanzu haka dai tuni aka yi jana’izar mamatan a ranar Lahadi a babban masallacin Juma’a na masarautar garin Tsafe.

Jihar Zamfara dai na cikin yankunan da ayyukan ƴan bindiga ke ci gaba da ta’azzara a jihohin Arewacin ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!