Labarai
Ƴan kasuwar sabon Gari sun bukaci Gwamnati ta samar musu da motar kashe Gobara
Kungiyar Kwankwasiyya Electronics Abubakar Rimi Market sun buƙaci Gwamnatin jihar Kano da ta samar musu da motocin kashe gobara domin gujewa matsala musamman ta tashin gobara a cikin kasuwa.
Shugaban ƙungiyar Magaji Umar Alkantara ne ya bayyana hakan yayin taron addu’a da ƙungiyar ta gabatar domin taya murnar samin nasara da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu a kotun ƙoli.
Ka zalika shugaban ya kuma nuna goyon bayan su bisa ga jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da bayar da haɗin kai domin samar musu da ci gaban kasuwar ta Sabon Gari.
Da yake jawabi ɗaya daga cikin dattawan kasuwar, Alhaji Sani Dankaka Mai Fanta ya bayyana kira yayi ga gwamnati wajen ƙara ingata harkar kasuwanci a kano da samarwa da matasa hanyoyin dogaro da kai.
- Da yake Jawabi ɗaya daga cikin Jagororin kungiyar, Muhammad Rabilu Ahmad wanda aka fi sani da Ustazun Kwankwasiyya ya bayyana cewar sun shirya wannan addu’a ne domin taya gwamna Abba Kabir Yusif murnar samin nasara da kuma tunatar da shi wajen samarwa da Al’ummar kano ci gaba a ɓangarori daban-daban na rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login