Labarai
Ƴan majalisa na duba ayyukan gwamnatin tarayya a Kano
Mambobin kwamitin ayyuka na majalisar wakilai ta tarrayya sun kai ziyara fadar gwamnatin Kano.
Shugaban kwamitin Abubakar Kabir Bichi ya ce sun kai ziyarar ne a wani ɓangare na zuwan su Kano tare da tawagar sa domin duba ayyukan hanyoyin da gwamnatin tarayya ke yi duba da muhimmancin su ga al’umma.
Ya ƙara da cewa, ayyukan da suka zo dubawa sun haɗa da aikin hanyar da ya tashi daga Abuja, Kaduna, Zariya, zuwa Kano, tare da hanyar Kano zuwa Maiduguri, da sauransu.
Kabir Bichi ya ce, zasu tabbatar ƴan kwangilar sun kammala ayyukan cikin lokacin da aka ɗibar wa aikin da kuma tuntuɓar su kan matsalolin da suke fuskanta domin magance su.
Da yake jawabi yayin karɓar su gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gode musu bisa ga wannan ƙoƙari, inda yace hakan zai taimaka wajen rage rasa rayuka da akeyi a manyan hanyoyin.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa gwamnan ya nemi ƴan kwamitin da su ja hankalin ƴan kwangilar wajen dagewa a kan ayyukan su sakamakon yanayin damina da ake ciki.
You must be logged in to post a comment Login