Labarai
Ƴan sanda sun ceto mutane 10 da aka sacesu a Kagarko

Rundunar ƴan Sandan jihar Kaduna, ta ce, jami’anta sun ceto mutane 10 da aka sace a yankin Kagarko na Jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Kaduna.
Sanarwar ta bayyana cewa, wasu ƴan bindiga kimanin 14 sun kai hari a ƙauyen Kushe Makaranta da ke ƙaramar hukumar Kagarko, inda suka sace wasu mazauna yankin suka tafi da su cikin dajin Rijana.
Rundunar ta ce bayan samun matsin lamba daga jami’an tsaro, ’yan bindigar sun tsere sun bar wadanda suka sace ɗin.
You must be logged in to post a comment Login