Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Yanzu-yanzu- An sake sakin daliban kwalejin Afaka da masu garkuwa da mutane suka sace

Published

on

 

 Yan bindigar da suka sace daliban kwalejin nazarin tsirrai da gandun daji 39 da ke Afaka a jihar Kaduna sun sake sakin dalibai biyar kwanaki uku da suka saki biyar daga cikin su.

Wannan dai ya kawo adadin dalibai 10 kenan suka saki cikin 39 wanda a yanzu akwai ragowar daliban 29 a hannun su.

Jaridar Daily Trust ta ce, Rahotanni sun bayyana cewa daliban da aka saki yanzu haka suna kan hanyar su ta zuwa asibiti don duba lafiyar su.

Cikin daliban da aka sako sun hadar da maza hudu da mace daya, wanda rundunar yan sanda ta samu nasarar ceto su a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!