Labarai
Ƴan sanda sun ceto mutane 187 daga hannun masu garkuwa da mutane
Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta miƙa sama da mutane 187 a hannun gwamnatin jihar, bayan sun kuɓutar da su daga masu garkuwa da mutane.
Mai magana da yawun rundunar Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, waɗanda aka ceto din sun haɗar da mata da maza har ma da ƙananan yara a cikin su.
Shehu ya kuma ce, bayan wasu ayyuka na musamman da aka gudanar a dajin Tsibiri da ke ƙaramar hukumar Maradun, an gano mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan Rini, Gora, Sabon Birni da Shinkafi a ƙananan hukumomin Bakura Maradun da kuma Shinkafi.
A cewar sanarwar tuni kwamishinan ƴan sandan jihar Ayuba Elkanah ya miƙa waɗanda aka ceto ga gwamna Muhammad Bello Matwalle, inda ya tabbatar masa cewa za a ci gaba da bincike.
You must be logged in to post a comment Login