Ƙetare
Ƴan sandan London sun tarwatsa waɗanda ake zargi da fashin Wayoyi

Ƴan sanda a birnin London sun ce, sun tarwatsa wata ƙungiyar barayi ta ƙasa da ƙasa da ta kware wajen safarar wayoyin salular jama’a da suka kwashe kimanin 40,000 tare da kai su zuwa China.
Magajin garin birnin Sadiq Khan, ya ce, ƴan sanda sun dirar wa shugabannin masu aikata laifukan ne ciki har da masu ƙwacen waya a kan tituna.
Aƙalla mutane 16 aka kama, a binciken da aka kwashe shekara guda ana yi.
Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa, tuni aka gurfanar da mutane uku, ciki har da ƴan Afghanistan da ake zargi da hannu a lamarin.
Haka kuma ta ƙara da cewa, ana tunanin suna sayar da kowacce waya guda ɗaya a kan kusan dalar Amurka 5000 saboda a buɗe suke, saɓanin wayoyin da ake sayarwa a China.
You must be logged in to post a comment Login