Manyan Labarai
Da yamamcin jiya Lahadi ne, Ministan shari’a kuma Antoni janaral Abubakar Malami SAN ya bar kasar zuwa Amurka don halatar taron yini 3 kan yadda hukumomin kasashen biyu ke aiki wanda za’a birnin Washington DC.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da maitaimaka masa kan harkokin yada labarai Dr, Umar Jibrilu Gwandu ya rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja ya sanya wa hannu a yau Lahadi cewar,ana kyautata zaton cewar ganawar zai maida hankali ne kan hanyoyi uku da yakamata a rataba hannu wajen kulla yarjejeniya da kasar nan da kuma tsibirin New Jersey da kasar Amurka kan yadda za’a dawo da Dala miliyan 321 da wasu suka wawure suka kuma jibge a can.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewar, Abubakar Malami zai sanya hannu ne a madadin Gwamnatin tarayya wajen ganin ba tare bata lokaci ba an maido wa Najeriya makudan kudaden da wasu tsirarun mutane suka sace tare jibigewa a kasar.
Bugu da kari a cewar sanarwar taron an saba yin sa duk shekara tsakanin Najeriya da Amurka kuma ana yin sa ne da zumar sake yin nazari kan karfafa fahimtar juna da kuma matakan da za’a bi wajen hanyoyin dufilomassiyya kan dai dawo da kudaden a tsakanin kasashen biyu.
Daga cikin kososhin gwamnati da zasu halaci taron akwai ministan kamfanoni, ciniki da zuba jari Otunba Adeniyi Adebayo da ministan tsaro majo janaral Bashir Magashi mai ritaya da ministan dake kula da harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama da baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Baba Gana Monguno mai ritaya da kuma ministan dake kula da ayyukan jin kai da kare ifitala’I da cigaban alumma Hajiya Sadiya Umar Faruq.