Connect with us

Labarai

Buhari ya sanya hannu kan dokar ‘yan sanda

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar ‘yan sanda ta majalisun dokokin tarayyar kasar nan suka sahale mata a kwanakin baya ta shekarar dubu biyu da ashirin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina.

Sanarwar ta ce shugaba Buhari ta cikin wata wasika da ya rubutawa majalisun dokokin tarayya ya bayyana cewa tuni ya sanya hannu kan dokar.

A cewar sanarwar sanya hannu kan dokar zai taimaka wajen kyautata ayyukan ‘yan sandan Najeriya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!