Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

NIMC ta rubaya kokarin ta wajen samar da katin shedar ‘yan kasa – Sarkin Kano

Published

on

Mai marataba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga hukumar yiwa katin ‘yan kasa rijista da su rubanya kokarin su wajen fadakarwa da wayar da kan al’umma da su fito suyi rijistar katin shaidar zama dan kasa saboda mahimmancin ta ga wasu ayyukan gwamnati.

Alhaji Aminu Ado Bayero na bayyana hakan ne a yayin da manyan jami’an hukumar suka kai masa ziyara karkashin jagorancin darakta mai kula da shiyyar Kano Alhaji Lawan Yahya yau a fadar sa.

Sarkin wanda yayi bayani mai tsayi game da mahimmancin mallakar katin shaidar zama dan kasa ga al’umma, yana mai cewa mallakar katin zai bada dama wajen shiga harkokin gwamnati da hukumomi a kasar nan.

A nasa jawabin daraktan shiyya na yin rijistar katin dan kasa anan Kano, Alhaji Lawan Yahya ya bukaci tallafin masarautar Kano, tare da bukatar masarautar ta umarci masu rike da masarautun gargajiya da su shiga cikin aikin ka’in-da-na’in.

A wani labarin kuma, mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi kungiyar mata masu tallafawa marayu da marasa karfi karkashin jagorancin shugabar kungiyar Hajiya Bilkisu Muhammad Rabi’u inda sarkin yayi maraba da ayuukan kungiyar da manufofinta.

Wakilin mu Muhammad Harisu Kofar Nasarawa ya rawaito cewa shugabar kungiyar ta ce kungiyarsu na tallafawa marayu da marasa karfi a cikin al’umma da nufin magance matsalolin talauci da kuncin rayuuwa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!