Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Published

on

Gwamnatin tarayya za ta yi wata ganawa da gamayyar kungiyoyin lafiya na kasar nan JUHESU.

Ganawar za ta mayar da hankali wajen tattauna batun tsunduma yajin aiki da JUHESU suka ƙudiri aniyar yi a faɗin ƙasar nan.

Wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ƙwadago da samar da aikin yi Mr Charles Akpan, ya fitar ce ta sanar da hakan.

A gobe Talata 7 ga watan Satumba za a gudanar da ganawar kamar yadda ministan ƙwadago Chris Ngige ya bada umarni.

Ngige ya ce, zai gana da shugabannin kungiyar, kan barazanar da suka yi na tsunduma yajin aiki a ranar 3 ga Satumba kan rashin biyan mambobin ƙungiyar kuɗaɗen su da sauran buƙatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!