Connect with us

Labarai

Muna dab da biyawa likitoci buƙatun su – Boss Mustapha

Published

on

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire sun bukaci likitoci masu neman ƙwarewa da su kwantar da hankalin su domin kuwa ana dab da biya musu bukatun su.

Boss Mustapha ya bayyana hakan a yayin da yake yiwa kwamitin yaki da cutar corona bayani a Abuja.

Ya ce, akwai bukatar likitoci masu neman ƙwarewa su yi duba kan halin da bangaren lafiya ke ciki a yanzu, wajen dawowa bakin aikin su.

Har ma ya ce, Najeriya na tsammanin karbar rigakafin cutar corona miliyan 52 a watanni shidan farko na shekarar 2022.

Da yake nasa jawabin ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire ya ce, tuni shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bukaci ƙungiyar ta janye yajin aikin da ta ke yi, har ma ya alkawarta biya musu bukatun su, sai dai har yanzu basu bi umarni ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!