Labarai
Al’ummar karkara su samar da Burtalai tsakanin makiyaya da manoma – Sarkin Kano
Al’ummar karkara su samar da Burtalai tsakanin makiyaya da manoma – Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Al’ummar karkara da su mayar da hankali wajen samar da burtalai tsakanin makiyaya da manoma.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin ziyarar da Kwamitin kula da burtalai na jihar Kano suka kai masa a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakimai da masu unguwannin har ma dagatai da su dinga sanya idanunsu wajen samar da burtalai a yankunan su musamman ma na karkara.
A nasa jawabin shugaban kwamitin kula da burtalai na jihar Kano Ibrahim Garba Muhammad yace sun je fadar ne domin neman albarka akan nauyin da gwamnatin Kano ta dora musu.
shugaban kwamitin ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su bi doka da oda wajen samar da burtalai a kananan hukumomin su.
You must be logged in to post a comment Login