Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya umarci iyayen kasa su sanya ido kan bakin fuska yayin zabe

Published

on

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci masu unguwanni da hakimai da har ma da dagatai da su kara sanya ido wajen shige da ficen bakin fuska lokacin zabe.

Sarkin ya bayar da umarnin ne a yau Juma’a, lokacin da yake jawabi ga manema labarai a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma bukaci al’ummar Kano da su fito su kada kuri’a a gobe kamar yadda doka ta tanada.

Haka kuma, Sarkin ya bukaci yan siyasa da su kauce wa sayen kuri’ar jama’a da kuma haifar da abinda zai janyo zubar da jini,.

Sarki Aminu Ado Bayero, ya kuma bukaci iyaye da su tsawatar wa yayansu kan su guje wa shiga hatsaniyar siyasa.

Haka Kuma Sarkin, ya yi kira ga limamai da su yi hudubarsu ta yau a kan zaman lafiya a tsakanin al’ummar Nijeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!