Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya na buƙatar kyakkyawan shugabanci – Atiku Abubakar

Published

on

Toshon mataimakin shugaban ƙasar nan Atiku Abubakar ya ce, Najeriya na buƙatar shugabanci da zai farfaɗo da tattalin arizkin ƙasa da ci gaban ta.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin kaddamar da wani littafi da shugaban kamfanin DAAR mamallakan gidan talabijin na AIT wanda Raymond Dokpesi ya wallafa.

Ya ce “ Najeriya na buƙatar kyakyawan shugaban ci da zai mayar da hankali wajen yaƙi da matsalolin tsaro da kuma dawo da walwalar jama’a.

Ko da aka tambaye shi kan cewa idan kuma shi ne mutumin da ya dace ya mulki Najeriyar a yanzu fa? Sai ya ce “Ko da ni ne na riga na faɗi ra’ayi na kan abin da nake gani daidai ne, kuma zan yi abinda ya kamata”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!